Isa ga babban shafi

Ba za mu goyi bayan Sweden ba saboda kona Qur'ani - Erdogan

Shugaban Turkiya Recep Tayyyip Erdogan ya ce, kasarsa ba za ta goyi bayan Sweden ba a kokarinta na neman kujerar mamba a Kungiyar Tsaro ta NATO sakamakon yadda wasu masu zanga-zanga suka kona Al’Qur’ani mai girma a birnin Stockholm.

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan
Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan AP - Emrah Gurel
Talla

Jim kadan da kammala ganawarsa da majalisar ministocinsa, shugaba Erdogan ya ce, wadanda suka bari aka yi wannan batancin a harabar ofishin jakadancinmu (a Stolkhom), kada su sa ran samun goyon bayanmu dangane da neman matsayi na mamba  a NATO.

A ranar Asabar ne aka gudanar da zanga-zangar nuna adawa ga Turkiya da kuma yunkurin Sweden na neman zama mamba a NATO, inda kuma aka kona kwafin Al’Qur’ani mai girma, lamarin da ya janyo zazzafan martani daga kasashen Larabawa.

Kasashen da suka yi tur da kona Qur’anin sun hada da Saudiya da Jordan da Kuwait, yayin da tuni gwamnatin Turkiya ta kira jakadan Sweden domin neman bahasi.

Sweden dai na bukatar goyon bayan Turkiya kafin cikar burinta na zama mamba a NATO, amma shugaba Erdogan ya yi wa kasar shagube, inda ya ce mata ta je ta nemi goyan bayan ‘yan ta’adda domin su ba ta kariya.

Tuni shugabannin Sweden suka yi tur da Rasmus Paludan, wani mai tsattsauran ra’ayi da ya jagoranci kona Al’Qur’anin mai girma a yayin zanga-zangar.

Sweden da Filand dukkaninsu na fafutukar samun kejerar mambobi a Kungiyar Tsaro ta NATO.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.