Isa ga babban shafi

Kasashe na maida martani game da rikicin Wagner da gwamnatin Rasha

Ana ci gaba da mayar da martani dangane da tada kayar-baya da shugaban kamfanin sojin hayar Wagner da dakarunsa suka yi wa gwamnatin Rasha a karshen makon da ya gabata, duk da cewa an samo masalaha a game da matsalar.

Kasashe na maida martani kan hatsaniyar da ta faru a Rasha a karshen mako.
Kasashe na maida martani kan hatsaniyar da ta faru a Rasha a karshen mako. AP - Olivier Matthys
Talla

A karshen makon da ya gabata ne dakarun hayar kamfanin Wagner suka fara tada kayar baya, tare da aniyar kawar da rundunar sojin Rasha bisa umurnin shugabansu, kuma tsohon babban abokin shugaba Vladimir Putin, hamshakin attajiri, Yevgeny  Prigozhin.

Jim kadan bayan fara wannan turjiya ta dakarun Wagner, fadar gwanatin Amurka ta fitar da sanarwar cewa shugaba Joe Biden ya gana da shugabanin Faransa, Jamus da Birtaniya a game barakar da aka samu a Rasha, inda bayan tattaunwarsu suka  jaddada goyon bayansu ga Ukraine.

Zalika,  ministocin harkokin wajen kasashen G7 sun yi wata ganawar gaggawa a game da wannan lamari da yake tamkar koma-baya a mamayar da Rasha ke wa Ukraine, wadda tun da farko suke adawa da ita.

Sai dai  a nasa bangaren shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, bayan ganawa ta wayar tarho da shugaba Putin na Rasha, ya  bayyana goyon bayansa gareshi, tare da aniyar ganin an lalubo masalaha.

Ita ko China, alwashi ta sha a game da tabbatar da zaman lafiya da dorewar kasa a Rasha, martaninta na farko kenan a game da tada-kayar baya na dan lokaci da Prigozhin da mayakansa na Wagner suka yi wa mahukuntan Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.