Isa ga babban shafi

Zelensky ya yaba da namijin kokarin sojojin sa bayan dakatar da harin Rasha a Kyiv

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya yaba wa rundunar sojojin saman kasar, bayan mummunan harin da aka kaiwa babban birnin kasar Kyiv, irin sa na farko tun bayan kaddamar da mamayar da Rasha ta yi.

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky. © via REUTERS / POOL
Talla

Harin da aka kai cikin dare da kuraman jirage, ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu tare da raunata wasu da dama.

Rasha ta kara matsa kaimi wajen kai hare-hare da jirage masu sarrafa kan su a babban birnin Ukraine a cikin wannan watan, tare da gargadin kasashen yammaci gameda sake ruru wutar rikicin bayan da Amurka ta amince ta baiwa Ukraine jiragen yaki samfurin F-16.

Volodymyr Zelensky ya ce a duk lokacin da sojojin saman kasar suka kakkabo kuraman jirage ko makamai masu linzami da Rasha ta harbo, rayuka da dama ne ke kubuta.

Wannan ne karo na 14 da kuraman jiragen yakin Rasha ke kaiwa babban birnin Ukraine Kyiv hari a cikin wannan watan kadai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.