Isa ga babban shafi

Manyan kasashe sun rubanya jarin da suke zubawa wajen samar da makamai

Manyan kasashen duniya da suka mallaki makaman nukiliya musamman China, sun rubanya jarin da su ke zubawa wajen samar da makamai, kuma a karo na uku kenan da su ke aikata haka a dai dai lokacin da tankiya ke tsananta a wasu yankuna na duniya. 

Wani nau'in makami mai linzami.
Wani nau'in makami mai linzami. AP
Talla

Wasu sabbin rahotanni biyu da aka fitar a wannan Litinin suka bayyana haka, inda suka ce manyan kasashen duniyar su tara sun kashe zunzurutun dala biliyan 82.9 wajen samar da makamai a bara kadai, inda Amurka ta kashe fiye da rabin wannan kudin ita kadai. 

Kungiyar  Kasa da Kasa mai fafutukar Kawo Karshen Makaman Nukiliya da kuma Cibiyar Bincike kan Zaman Lafiya ta Duniya da ke Stockholm, su ne suka fitar da rahotannin guda biyu. 

Daya daga cikin rahoton ya nuna cewa, adadin harsashen makaman nukiliya da kasashen Birtaniya da China da Faransa da India da Isra’ila da Korea ta Arewa da Pakistan da Rasha da Amurka suka mallaka ya ragu daga dubu 12 da 710 da suke da su a 2022 zuwa 12, 512 a farkon wannan shekara. 

Sai dai yanu haka wadannan kasashe sun kebe wasu daga cikin makaman na nukilya da ke cikin shirin-ko-ta-kwana, yayin da dubu 9 da 576 ke ajiye a rumbun sojoji da za a iya harba su kowane lokaci, abin da ke nufin cewa, an samu karin fiye da 86 na makaman da kasashen suka tanada a shekarar 2021. 

China ce ke kan gaba wajen habbaka rumbunta na adana makaman nukiliya, inda adadin harsashen nukiliyarta ya tashi daga 350 zuwa 410 a yanzu. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.