Isa ga babban shafi

Adadin mutanen da guguwar Mocha ta kashe a Myanmar ya kai 81

Alkaluman mutanen da suka mutu sakamakon kakkarfar guguwar Mocha a Myanmar ya karu zuwa mutum 81 dai dai lokacin da tarin al’ummar kauyukan da ibtila’in ya shafa ke tattaruwa waje daya a wani yunkuri na neman agajin matsugunan wucin gadi daga mahukunta.

Yadda  kakkarfar guguwar Mocha ke ci gaba da barna a Myanmar.
Yadda kakkarfar guguwar Mocha ke ci gaba da barna a Myanmar. via REUTERS - OBTAINED BY REUTERS
Talla

Tun a karshen mako da ya gabata kakkarfar guguwar mai gudun kilomita 195 a sa’a guda da aka yiwa lakabi da Mocha ta isa wasu kauyukan Myanmar da ke gabar ruwa inda ta rushe tarin gidaje yayinda ta ke ci gaba da barna a sassan yankin.

Jami’aisunceakwaifargabaradadinmamatanzaiiyakaruwa, la’akari da cewarakwaiwasumutanenfiye da 100 da sukabace.

Guguwar hade da kakkarfan ruwan sama ta rika awon gaba da gidajen kauyukan baya ga kwaye rufun wasu, lamarin da ya raba daruruwan jama’a da muhallansu.

 KididdigatanunaIftila’inyalakumerayukanmutane 46 a wasukauyukanjiharRakhinekadai sai wasu 13 a Rathedaung, baya gawasugwammanrayukan da sukasalwanta a wasuyankunan na jihar ciki har da Sittwefadar gwamnatin jihar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.