Isa ga babban shafi

Kasashen Kudancin Asiya sun nuna damuwa kan rikicin Myanmar

Kasashen kudu maso gabashin Asiya sun bayyana damuwa matuka dangane da tashin hankalin kasar Myanmar, tare da yin Allah wadai da harin da aka kai kan ayarin jami’an diflomasiyya da ke kai agajin jin kai a kasar.

Tutar kasashen Kudu Maso Gabashin Asiya ASEAN inda ake taron kungiyar na wannan shekara a Jakarta na kasar Indonesia. 9/05/23
Tutar kasashen Kudu Maso Gabashin Asiya ASEAN inda ake taron kungiyar na wannan shekara a Jakarta na kasar Indonesia. 9/05/23 AP - Achmad Ibrahim
Talla

Kungiyar ASEAN ta jagoranci yunƙurin diflomasiyya na warware rikicin na Myanmar, amma ƙoƙarin da ta yi ya zuwa yanzu ya kasa shawo kan zubar da jini da ya samo asali tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a shekarar 2021.

Rikicin da ake fama da shi a kasar Myanmar karkashin mulkin soja ya mamaye tattaunawar da ake yi a taron kungiyar kasashen kudu maso gabashin Asiya a wannan mako a kasar Indonesiya, yayin da kungiyar kasashen yankin ke fuskantar suka kan gazawarta wajen kawo karshen rikicin.

Gwamnatin mulkin sojan dai ta yi watsi da sukar da kasashen duniya ke yi mata, sannan ta ki yin hulda da ‘yan adawa da suka hada da korarrun ‘yan majalisar dokokin kasar, da masu adawa da juyin mulkin, da kuma kungiyoyin ‘yan tsiraru masu dauke da makamai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.