Isa ga babban shafi

Isra'ila da Islamic Jihad sun yi wa juna ruwan makaman roka cikin dare

Sojojin Isra’ila da mayakan Islamic Jihad a yankin Gaza sun sake shafe tsawon dare suna kaiwa juna hare-haren manyan makamai dai dai lokacin da alkaluman Falasdinawan da aka kashe cikin kwanaki 2 da faro rikicin ke tasamma 22.

Isra'ila ta ce Islamic Jihad ta harba mata makamai fiye da 400.
Isra'ila ta ce Islamic Jihad ta harba mata makamai fiye da 400. AP - Ohad Zwigenberg
Talla

Rikicin wanda ke matsayin mafi muni da aka gani tsakanin bangarorin biyu a watannin baya-bayan nan kowanne bangare na ci gaba da harba makaman roka ta yadda babu abin da ake jiyowa sai karar harbawa da kuma tarwatsewarsu, kamar yadda majiyoyin labaran da ke sanya idanu kan rikicin ke bayyanawa a wani yanayi da Masar ke shige da fice don ganin ta sulhunta mayakan na zirin Gaza da Isra’ila.

Kungiyar Islamic Jihad ta bayyana kisan guda cikin kwamandojinta da ke jagorantar sashen harba makaman roka Ali Ghali wanda ta ce na kashe shi a zirin na Gaza tare da wasu mayaka.

Isra’ila ta sanar da cewa hare-harenta na baya-bayan nan ta kaisu ne kan sashen harba makaman rokan na Islamic Jihad wanda ya kashe tarin mutane, bayan da ministan tsaron Isra’ila Yoav Gallant ya bayyana cewa na harbo musu makaman fiye da 400 daga jiya laraba zuwa yau alhamis.

A cewar ministan wannan mataki na Islamic Jihad da kuma barnar da hare-haren ke yi musamman a kudancin Isra’ila ya sanya su ci gabar da farmakar sashen harba makamai na kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.