Masar za ta zuba dala miliyan 500 wajen sake gina Gaza da Isra'ila ta rusa
Gwamnatin Kasar Masar tayi tayin bada agajin Dala miliyan 500 domin sake gina birnin Gaza da hare haren bama baman Israila ya yiwa matukar illa.
Wallafawa ranar:
Fadar shugaban kasa AbdelFatah al Sisi ta sanar da gudummawar tare da bayar da gudumawar kwararrun kamfanonin maginan da za suyi aikin.
Tsawon kwanaki Sojin Isra'ila suka shafe suna harba makaman roka baya ga bama-bamai ga yankin na Gaza, wanda ya hallaka tarin fararen hula ciki har da kananan yara, ko da ya ke Isra'lian na ci gaba da ikirarin cewa ta na kaddamar da farmakin ne kan mayakan Hamas.
Masar ta yi ta kokarin ganin ta sasanta Isarila da Falasdinawa domin kawo karshen tashin hankalin da ke gudana a tsakanin su amma abin yaci tura a fadan da ya barke tun ranar 10 ga wannan wata.
Kasar ta kuma aike da tan 65 na magunguna domin taimakawa wadanda suka jikkata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu