Isa ga babban shafi
Falasdinawa - Isra'ila

Lamurra na cigaba da tsananta a birnin Gaza

An samu karin hasarar rayuka a birnin Gaza sakamakon cigaba da kai hare-haren da Isra’ila ke yi kan Falasdinawa, farmakin da a yau Lahadi ya shiga rana ta bakwai.

Tankar yakin Isra'ila yayin harba bama bamai kan birnin Gaza daga kan iyaka da Isra'ila,
Tankar yakin Isra'ila yayin harba bama bamai kan birnin Gaza daga kan iyaka da Isra'ila, AP - Ariel Schalit
Talla

Rahotanni sun ce da sanyin safiyar yau din Falasdinawa akalla 4 suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata, yayin farmakin da jiragen Isra’ilar suka kai kan wasu wasu dogayen gine-gine da suka rusa.

Yadda mayakan Falasdinawa na kungiyar Hamas ke harba makaman roka kan Isra'ila daga birnin Gaza.
Yadda mayakan Falasdinawa na kungiyar Hamas ke harba makaman roka kan Isra'ila daga birnin Gaza. AP - Hatem Moussa

A can Birnin Tel Aviv dake Isra’ila kuwa, mutane ne suka rika rugawa zuwa cikin gine-ginen samun kariya daga hare-haren mayakan kungiyar Hamas dake cigaba da harba daruruwan rokoki kan su, yayin da rundunar sojin kasar ta harba na’urori kakkabo makaman rokar Falasdinawan.

Sake tsanantar rikicin dai na zuwa ne sa’o’i kalilan bayan harin da Isra’ila ta kai kan wani sansanin ‘yan gudun hijira a birnin Gaza, inda ta kasha fararen hula 10 ciki har da yara kanana 8, yayin da kuma ta rusa ginin da ya kunshi ofisoshin kafafen yada labarai, ciki har da na kamfanin dillancin labarai na AP da kuma na kafar talabijin ta Aljazeera duk dai a birnin na Gaza.

Wasu sassan birnin Gaza da jirage yakin Isra'ila suka kaiwa farmaki.
Wasu sassan birnin Gaza da jirage yakin Isra'ila suka kaiwa farmaki. AP - Adel Hana

Cikin wani jawabi da ya gabatar ta kafar talabijin din kasar a daren jiya Asabar, Fira Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya s ha alwashin cigaba da kai hare-hare kan Gaza har sai abinda hali yayi, yayin da shi kuma jagoran mayakan Falasdinawa na kungiyar Hamas, Isma’ila Haniya ya lashi takobin cewar babu gudu ba ja da baya.

Kawo yanzu Falasdinawa akalla 149 cikinsu har da yara 41 suka rasa rayukansu a birnin Gaza, yayin da wasu kimanin 950 suka jikkata a tsawon mako guda da barkewar rikici tsakanin Isra’ila da Falasdinawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.