Isa ga babban shafi

Majalisar Dinkin Duniya ta koka a kan yawaitar tserewar fursunoni a Sudan

Majalisar dinkin duniya ta koka a kan yadda ake cigaba da samun fashe fashen gidajen yari a Sudan da a halin yanzu ake fama da rikice rikice, matakin da yayi sanadiyar tserewar manyan masu laifin yaki daga gidajen kason.

Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres
Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres AP - SALVATORE DI NOLFI
Talla

Yayin zantawarta da manema labnarai a birnin Geneva, kakakin kungiyar Ravina Shamdasani ta ce sun shiga damuwa sosai saboda tserewar wadannan fursunonin, la’akari da cewa hakan ka iya rura wutar rikicin da ake kokarin kashewa a halin yanzu.

Kalaman na Shamdasani na zuwa ne bayan da aka samu ghidajen yari da dama da aka fasa cikinsu har da babban gidan kason da aka tsaren manyan masu laifin yaki.

MDD ta kuma ce rikicin na sudan na kara rura rikicin kabilanci a yankin yammacin birnin darfur wanda a sanadiyar hakan aka samu asarar rayuka kusan 100 a cikin ‘yan kwanaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.