Isa ga babban shafi

Farkon shekarar 2023 ya fi kowane lokaci muni ga 'yan ci rani - Rahoto

Majalisar dinkin duniya ta bayyana watanni uku na farkon wannan shekara ta 2023, a matsayin lokaci mafi muni ga bakin haure da ke fafutukar tsallaka tekun Meditaraniya don shiga Turai tun shekarar 2017. 

Wasu 'yan ci rani da ke son tsallaka tekun Meditaraniya don shiga nahiyar Turai.
Wasu 'yan ci rani da ke son tsallaka tekun Meditaraniya don shiga nahiyar Turai. REUTERS - AYMAN AL-SAHILI
Talla

Cikin rahoton da ta fitar a ranar Laraba, hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce daga farkon watan Janairu zuwa Maris a shekarar  bana kadai rayukan ‘yan ci rani akalla 441 suka salwanta, a yayin da suke kokarin tsallaka teku zuwa Turai, akwai kuma yiwuwar adadin ya zarce haka. 

Hukumar ta IOM ta kara da cewar jinkirin da ake samu wajen gudanar da ayyukan ceto a karkashin jagorancin gwamnati ya taka rawa wajen haddasa hasarar dimbin rayukan da aka gani a hadurran da suka rutsa da ‘yan ci ranin da ke hankoron tsallaka teku daga arewacin Afrika don zuwa Turai. 

Shugaban IOM Antonio Vitorino ya ce bai kamata a cigaba da jan kafa wajen daukar matakan kawo karshen hasarar dimbin rayukan bakin haure a tekun Meditarniya ba, wanda kididdiga ta nuna cewar ‘yan ci ranin fiye da dubu 20 ne suka mutu a cikinsa, daga shekarar 2014 zuwa yanzu. 

Yanzu haka dai hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya na kan gudanar da bincike akan bacewar da ‘yan ci rani masu yawan gaske suka yi a tekun na Meditaraniya a lokuta da dama, ba kumma tare da an gano gawarwakinsu ba, ballantana a sa ran an gudanar da aikin ceto wasu daga cikinsu. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.