Isa ga babban shafi

Akalla mutane bakwai suka mutu a wata gobara a kusa da birnin Manila

Mutane 7 da suka hada da yara biyu sun mutu a wata gobara da ta tashi da yammacin jiya asabar a kusa da babban birnin kasar Philippines kamar dai yada ‘yan sanda suka ruwaito.

Wasu daga cikin unguwanin birnin Manilla
Wasu daga cikin unguwanin birnin Manilla © AP/Aaron Favila
Talla

Gobarar ta lalata gidaje 40 a karamar hukumar Taytay mai yawan jama'a a kudu maso gabashin Manilai.

Iyalai da dama, wadanda ke zaune a gida daya da ake iya samun damar shiga ta wani dogon lungu da sako, sun kone cikin wuta.

Wadanda abin ya shafa sun hada da wata yarinya ‘yar shekara biyu da wani yaro dan shekara 12.

"Ba su sami damar tserewa ba.in ji shugaban 'yan sandan Taytay Joel Custodio ga AFP. "An same su suna rungume da juna."

‘Yan sanda sun kara da cewa akalla mutum daya ya ji rauni sakamakon fadowar tarkace.

Gobarar ta yi barna a kalla iyalai 60, a cewar ‘yan sanda.

An dauki kusan sa'o'i biyu kafin a kashe gobarar, in ji Custodio, za su gudanar da binciken da ya dace,har idan ta kama za a hunkuta masu hannu a wannan kazamin aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.