Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun kashe wani gwamna da mutane 5 a Philippines

Wasu ‘yan bindiga dadi sun harbe gwamnan lardin Negros da ke kasar Philiphines Roel Degamo tare da karin wasu mutane biyar, a wani hari na baya-bayan nan da aka kai wa "yan siyasa. 

Taswirar Philippines.
Taswirar Philippines. AFP
Talla

Jami’an ‘yan sanda sun ce ‘yan bindigar su 6 rike da manyan bidigogi sanye da kakin sojoji sun kustsa gidan Gwamnan ne a yankin Pamplona tare da bude wuta. 

Ko da yake tabbatar da faruwar lamarin, magajin garin Pamplona Janice Degamo ya ce Gwamna Roel bai chanchanci irin wannan mutuwa ba la’akari da yadda ya dage wajen ganin ci gaba al’ummar da yake jagoranta ba dare ba rana. 

A Karin bayanin da ‚yan sanda suka yi, sun ce bayan mutane 6n da suka mutu sanadin harin, akwai kuma wasu da ke asibiti, kuma kawo yanzu babu tabbaci game da yiwuwar ceto rayuwar su. 

Degamo mai shekaru 56 shine jami‘in gwamnauti na uku da ‚yan bindiga suka hallaka, tun bayan zabukan kasar da aka gudanar a bara. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.