Isa ga babban shafi

Jirgin sama dauke da mutane hudu ya yi hatsari a kasar Philippines

Wani karamin jirgin sama dauke da mutane hudu ya yi hatsari a tsakiyar kasar Philippines inda masu aikin ceto ke neman wadanda suka tsira, kamar dai yada wani jami’in kula da harakokin sufurin jiragen sama ya sanar.

Hatsarin jirgin sama dauke da fasinjoji
Hatsarin jirgin sama dauke da fasinjoji AFP - -
Talla

Hukumar kula da sufurin Jiragen sama ta Philippines (CAAP) ta fitar da sanarwa inda ta ce jirgin Cessna mai lamba 340 ya bace ne da sanyin safiyar jiya asabar bayan ya tashi zuwa Manila daga filin jirgin saman Bicol da ke kudancin babban birnin kasar.

Hukumar kula da harakokin jiragen ta kara da cewa jirgin na dauke da fasinjoji biyu, matukin jirgi da ma'aikaci daya.

Wani jami'in hukumar CAAP Eric Apolonio ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa matsalar ita ce yanayi mara kyau kuma yana kawo cikas ga yanayin binciken kasa."

Hatsarin jirgin ya zo ne kasa da wata guda bayan wani jirgin saman Cessna ya bace a ranar 24 ga watan Janairu a lardin Isabela da ke arewacin kasar. Ana ci gaba da neman tarkacen jirgin.

A wani lamari na daban kuma, an kashe wasu ma’aikatan jirgin sama biyu na kasar Philippines a wani atisayen horo a watan da ya gabata lokacin da jirginsu mai lamba SF260 Marchetti ya fado kan wani katafaren gonar shinkafa a lardin Bataan, kusa da Manila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.