Isa ga babban shafi

Wata mahaukaciyar guguwa ta aukawa kasar Philippines

Philippines na cikin shirin ko ta kwana yayin da wata mahaukaciyar guguwa mai karfin gaske ta fara afkawa tsibiran gabashin kasar.

Hukumomin kasar sun ce guguwar na gudun wuce sa'a da ba a taba ganin irin ta ba
Hukumomin kasar sun ce guguwar na gudun wuce sa'a da ba a taba ganin irin ta ba © AP - Kyodo
Talla

Masu hasashen yanayi sun ce mahaukaciyar guguwar Noru tana daukar iskar da ta kai kilomita 240 a cikin sa’a guda, bayan da ta afkawa tsibiran Polillo kuma ta nufi yamma zuwa tsibirin Luzon.

Bayanai sun ce guguwar na iya haifar da ambaliyar ruwa,  zabtarewar kasa, a sassan kasar, ciki har da babban birnin kasar, Manila.

Tuni aka bukaci mutanen da ke wurin da ke tattare da hadari da su yi gaggawar ficewa.

Guguwar ta karu da kilomita 90 kan kowacce sa’a guda a cikin sa'o'i 24. Wani mai hasashen yanayi Robb Gile ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa karin gudun da aka gani abu ne da ba a taba ganin irinsa ba.

Bayanai daga kasar na cewa yanzu haka an dakatar da zirga-zirgar jiragen sama.

Kimanin mutane 400 ne suka mutu a lokacin da guguwar Rai ta afkawa kasar a watan Disambar 2021.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.