Isa ga babban shafi
Philippines - Guguwa

Guguwa ta raba mutane fiye da dubu 300 da muhallansu a Philippines

Jami'an agajin gaggawa a Philippines sun ce adadin wadanda da suka mutu sakamakon kakkarfar guguwa da ta afkawa wasu sassan kasar ya karu daga mutane 33 zuwa 75.

Yadda guguwar Rai ta tafka barna a wasu yankunan kasar Philippines.
Yadda guguwar Rai ta tafka barna a wasu yankunan kasar Philippines. Alan TANGCAWAN AFP
Talla

Guguwar da kwararru suka yi wa lakabi da Rai, zalika suka bayyana ta a matsayin mafi muni cikin shekarar 2021 a kasar ta Philippines, ta afkawa yankunan kudanci da tsakiyar wasu tsibirai ne cikin gudun kilomita 195 a sa’a 1, inda kawo yanzu ta raba mutane fiye da dubu 300,000 da muhallansu gami da tumbuke manyan turakun lantarki da bishiyoyi.

Wata babbar bishiya da guguwar Rai ta tumbuke a kasar Philippines.
Wata babbar bishiya da guguwar Rai ta tumbuke a kasar Philippines. Alan Tangcawan AFP

Duk da cewa daga bisani guguwar ta rage gudun da take yi  zuwa kilomita 150 cikin sa’a 1, iskar ta zubar da ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya mamaye kauyuka, gami da rushe gine-ginen a yankunan da ta ratsa.

A halin yanzu dai jami’ai sama da dubu 18, da suka hada da sojoji da 'yan sanda da masu gadin bakin ruwa da kuma jami'an kashe gobara ne suka dukufa wajen aikin ceto a yankunan da iftila’in guguwar Rai da kuma ambaliyar ruwa ya fi kamari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.