Isa ga babban shafi

Sabuwaar girgizar kasa ta hallaka mutane 5 a Philippine

Akalla Mutane 5 sun mutu sakamakon rugujewar gine-gine 2 sanadiyyar wata kakkarfar girgizar kasa da ta dirarwa wani yanki na kasar Philippines.

Wasu jami'an agaji a yankin da aka fuskanci girgizar kasa
Wasu jami'an agaji a yankin da aka fuskanci girgizar kasa 路透社
Talla

Rahotanni sun ce an yi nasarar zaro mutane 3 da ginin ya danne su a kauyen Porac, haka zalika wata tsohuwa da jikanta wadanda suma wani ginin na daban ya hallaka a Lubao.

Gwamnan yankin Pampanga da ya fuskanci girgizar kasar Lilia Pineda ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce tuni jami’an agaji suka shiga aikin ceto.

A cewar Gwamnar tun da tsakaddaren jiya ne girgizar kasar ta fara wadda ta ce ta haddasa tsoro a zukatan al’ummar yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.