Isa ga babban shafi
Philippines - ICC

ICC za ta binciki yakin da Philippines ta kaddamar kan 'yan kwaya

Kotun hukunta manyan laifuffuka da ke birnin Hague ta bada umurnin gudanar da bincike akan yakin da kasar Philippines ta kaddamar kan masu mu’amala da miyagun kwayoyi abinda yayi sanadin rasa dimbin rayuka.

Shugaban kasar Philippine Rodrigo Duterte.
Shugaban kasar Philippine Rodrigo Duterte. LISA MARIE DAVID POOL/AFP
Talla

Alkalan kotun sun ce akwai shaidun da ke nuna cewar an tafka kura-kurai wajen take hakkin Bil Adama wajen gudanar da yakin, wanda yayi sanadin halaka dubban mutane.

Shugaban kasa Rodrigo Duterte ya janye kasar daga cikin kotun a shekarar 2019 bayan ta kaddamar da bincike akan irin wuce gona da iri da hukumomin kasar suka yi wajen yaki da shan kwayoyin.

A shekarar 2016 aka zabi shugaba Duterte bayan da yayi alkawarin kawar da matsalar miyagun kwayoyi a Philippines, in da ya baiwa 'yan sanda umarnin kashe wadanda ake zargi da tu'ammuli da miyagun kwayoyi.

Akalla mutane dubu 6 da 181 aka kashe tun daga watan Yulin shekarar 2016, kamar yadda kididdigar hukumomin Philippines suka fitar a watan Yulin bana.

Sai dai masu gabatar da kara na kotun ICC, sun kiyasta cewa adadin mutanen da aka kashe ya kai tsakanin dubu 12 zuwa dubu 30 da sunan yaki da 'yan kwaya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.