Isa ga babban shafi
Philippine -zabe

Marcos junior dan tsohon shugaban Philippine ya lashe zaben kasar

Ferdinand "Bongbong" Marcos Junior dan tsohon dan kama karyar Philippine marigayi Ferdinand Marcos ya yi nasarar lashe zaben kasar da gagarimin rinjayen, bayan da al’umma suka yi watsi da gargadin masana kan yiyuwar zaben matashin dan siyasar ya shafi tattalin arziki da demokradiyyar kasar.

Bongbong Marcos dan tsohon shugaba marigayi Ferdinand Marcos.
Bongbong Marcos dan tsohon shugaba marigayi Ferdinand Marcos. AP
Talla

Dai dai lokacin da ake gab da Karkare kidayar kuri’un da aka kada a zaben, alkaluma sun nuna cewa Marcos Junior na da jumullar kashi 56 na kuri’un, fiye da ninkin yawan kuri’un da babban abokin adawarshi Leni Robredo na Librel ya samu.

Zuwar yanzu Ferdinand Bongbong Marcos Junior na da kuri’u miliyan 16 da doriya nasarar da ke shirin kawo karshen shekaru 6 na mulkin shugaba Rodrigo Duterte tare da kuma da komawar mulkin kasar karkashin iyalin Marcos bayan shekaru fiye da 30.

Masana na ganin komawar mulki karkashin iyalin Marcos tsohon dan kama karyar kasar ta Philippine zai kassara demokradiyyar kasar tare da mayar da kasar cikin matsalar cin hanci da rashawa kamar yadda ya faru a lokacin mulkin Marcos.

Al’ummar Philippine na ganin Marcos Junior zai taka muhimmiyar rawa wajen fitar da kasar daga kangin talaucin da ta fada tun bayan shudewar mulkin mahaifinshi, yayinda a wani zabe na daban kuma al’ummar kasar suka kadawa ‘yar shugaba Duterte kuri’a a matsayin mataimakiyar shugaban kasa.

A shekarar 1986 ne maroigari shugaba Marcos ya tsere daga Philippine bayan wani juyin juya halin da boren jama’a da ya hambarar da kujerar mulkinsa biyo bayan tsanantar zarge-zargen rashawa da cin hanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.