Isa ga babban shafi
Philippines-Guguwa

Adadin mutanen da kakkarfar guguwa ta hallaka a Philippines ya kai 388

Alkaluman gwamnatin Philippines ya nuna yadda mutane 388 suka mutu a kakkarfar guguwar da ta afkawa kasar mafi muni a shekarun baya-bayan nan.

Dubunnan mutane ne yanzu haka ke rayuwa a sansanonin wucin gadi da gwamnatin kasar ta samar.
Dubunnan mutane ne yanzu haka ke rayuwa a sansanonin wucin gadi da gwamnatin kasar ta samar. AP - Jay Labra
Talla

Guguwar wadda aka yiwa lakabi da Rai ta afkawa kudanci da tsakiyar kasar ta Asiya ne a ranakun 16 da 17 ga watannan inda ta haddasa katsewar lantarki da datsewar manyan hanyoyi baya rushe dubunnan gidaje.

Kafin yanzu hukumar ‘yan sandan kasar ta Philippines ta ce mutane 375 suka rasa rayukansu kafin sabbin alkaluman Ofishin kula da al’amuran ‘yan kasa da ke sanar da alkaluman mutanen 388 matsayin wadanda guguwar ta sabbaba mutuwarsu.

Alkaluman sun kuma nuna yadda wasu mutum 60 suka yi batan dabo bayan zanga-zangar wadda ta shafi karuruwa 430 na cikin kasar tare da rushe gidaje fiye da dubu 482.

Wasu bayanai sun nuna cewa yanzu haka akwai mutane miliyan 4 da ke bukatar daukin gaggawa bayan tagayyara daga guguwar ta Rai.

Yanzu haka akwai mutane fiye da dubu 300 da ke rayuwa a sansanonin wucin gadi da gwamnati ta samar yayinda wasu fin dubu 200 na daban rabe a kodai gidajen ‘yan uwa ko na abokanan arziki.

Guguwar ta Rai ita ce mafi muni da Philippines ta gani bayan Haiyan da ta hallaka mutane dubu 7 da 300 a shekarar 2013.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.