Isa ga babban shafi

Saudiyya da Iran sun sha alwashin tabbatar da tsaro a Gabas ta Tsakiya

Manyan jami'an diflomasiyyar kasashen gabas ta tsakiya Iran da Saudi Arabiya sun gana a birnin Beijing, inda suka yi alkawarin yin aiki tare don samar da tsaro da kwanciyar hankal" a yankinsu mai cike da rudani, bayan wata yarjejeniyar ba zata da China ta kulla.

Ministan harkokin wajen Iran Hossein Amirabdollahian, daga dama, yayin ganawa da takwaransa na Saudiyya Faisal bin Farhan Al Saud a birnin Beijing, ranar 6 ga Afrilu, 2023.
Ministan harkokin wajen Iran Hossein Amirabdollahian, daga dama, yayin ganawa da takwaransa na Saudiyya Faisal bin Farhan Al Saud a birnin Beijing, ranar 6 ga Afrilu, 2023. AP
Talla

A wata sanarwar hadin gwiwa da aka fitar bayan tattaunawa tsakanin ministan harkokin wajen Iran Hossein Amir-Abdollahian da takwaransa na Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan, bangarorin biyu sun sha alwashin ci gaba da yin aiki tare don kyautata alaka.

Sanarwar ta kara da cewa, sassan biyu sun jaddada muhimmancin bin diddigin aiwatar da yarjejeniyar birnin Beijing da kuma yadda za a fadada shirin amincewa da juna da kuma fannin hadin gwiwa da kuma taimakawa wajen samar da tsaro, kwanciyar hankali da wadata a yankin Gabas ta Tsakiya.

Gwamnatocin Tehran da Riyadh sun sanar da yarjejeniyar da Beijing ta kulla a watan Maris don maido da dangantakar da ta yanke shekaru bakwai da suka gabata, lokacin da masu zanga-zanga a Iran suka kai hari kan ofisoshin diflomasiyyar Saudiyya.

Ziyarar ministocin a birnin Beijing ta zo ne a daidai lokacin da shugaban Faransa Emmanuel Macron da shugabar kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen su ma ke ziyara a babban birnin kasar ta china, inda suke neman ganin an kawo karshen rikicin Ukraine.

Gyara alaka tsakanin Saudiyya mai rinjayen mabiya sunni, wato babbar mai fitar da man fetur a duniya, da Iran mai rinjayen mabiya mazhabar Shi'a, kasar da ta kasance tana takun saka da gwamnatocin kasashen yammacin duniya kan ayyukanta na nukiliya, suna da damar sake fasalin dangantaka a yankin da ke fama da tashe-tashen hankula shekaru da dama.

Sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar ta ce bangarorin biyu sun yi shawarwari tare da yin musayar ra'ayi tare da mai da hankali kan batun maido da huldar da ke tsakaninsu a hukumance da kuma matakan da za a dauka na sake bude ofisoshin jakadancinsu.

Ana sa ran tattaunawar ta ministocin harkokin wajen kasashen biyu, za ta biyo bayan ziyarar da shugaban kasar Iran Ibrahim Raisi zai kai birnin Riyadh.

Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Mohammad Mokhber ya bayyana a ranar Litinin cewa, Raisi ya karbi goron gayyata daga Sarki Salman na Saudiyya.

Nasarar da kasar China ta samu wajen hada kasashen Iran da Saudiyya sun kalubalanci matsayin da Amurka ta dade tana yi a yankin gabas ta tsakiya.

Wakilai daga kasashen Iran da Saudiyya sun yi tataunawa da dama a Bagadaza da Oman kafin su gana a birnin Beijing na kasar ta China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.