Isa ga babban shafi

Manyan kasashen Duniya sun kalubalanci Iran kan shirinta na nukiliya

Amurka ta fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa tare da Faransa da Birtaniya da Jamus a jiya Juma'a inda suka yi suka kan rashin aiki da bin umurni da Iran ta yi kan rahoton da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ta fitar kan shirinta na nukiliya.

Tambarin Nukuliya
Tambarin Nukuliya REUTERS/Francois Lenoir
Talla

Hukumar da ke sa ido kan makamashin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi ga hukumomin Tehran bayan ta gano cewa an samu sauye-sauye ba tare da sanar da masana'antar sarrafa makamashi ta Fordo ba kan na'urorin da za su iya wadatar da sinadarin Uranium zuwa kashi 60 cikin dari.

Iran ta yi ikirarin cewa wani babban jami'in hukumar ta IAEA ya yi kuskure ya nuna cewa ba a bayyana sauye-sauyen ba, kuma daga baya aka warware matsalar.

Sanarwar ta hadin gwiwa ta ce "Ikrarin Iran na cewa an aiwatar da wannan mataki cikin kuskure bai isa ba."

A cewar rahoton na IAEA, wanda kamfanin dillancin labaran AFP ya gani, a yayin wani bincike na Fordo ba tare da sanarwa ba a ranar 21 ga watan Janairu, masu binciken sun gano cewa "kuskuren IR-6 centrifuge cacades suna da alaƙa da juna ta hanyar da ta sha bamban da yanayin aiki da Iran ta ayyana zuwa hukumar."

Hukumar ta IAEA ba ta fayyace irin sauye-sauyen da aka yi ga cudanya tsakanin tarkace ba.

Kasashen hudu sun bayyana cewa, wannan sauyin ya saba wa matakin da aka cimma tsakanin Iran da hukumar a karkashin yarjejeniyoyin da aka kulla, kuma "irin wannan rashin sanarwar da ake bukata na kawo cikas ga ikon hukumar na ci gaba da gano makaman nukiliyar Iran a kan lokaci."

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.