Isa ga babban shafi

Sauyin yanayi na dakile kokarin kasashe wajen yakar illar da ya haifar- MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa matsalolin da sauyin yanayi ke haifarwa a kasashe da dama, na barazanar fin karfin matakan da ake dauka wajen dakile karfin da tasirin dumamar yanayin ke ci gaba da yi akan muhallin dan Adam.

Sauyi ko dumamar yanayi na matsayin babban kalubale ga wanzumar tsirrai da sauran halittun ban kasa.
Sauyi ko dumamar yanayi na matsayin babban kalubale ga wanzumar tsirrai da sauran halittun ban kasa. REUTERS - THOMAS PETER
Talla

Gargadin na Majalisar Dinkin Duniya ya zo ne a dai dai lokacin da tallafin kudaden hukumomin kasa da kasa ke bayarwa don yaki da dumamar yanayi ya ragu sau goma kasa da abin da ake bukata.

Yawancin kasashe masu tasowa da ba su da hannu wajen haddasa dumamar yanayi na cikin wadanda suka fi fuskantar masifun da matsalar ke haifarwa, da suka hada da karuwar fari, ambaliya ruwa da kuma fuskantar kakkarfar guguwar da ke kacaccala akasarin yankunan da ta afkawa.

Bayar da kudade don taimakawa kasashe marasa karfi wajen rage kaifin tasiri matsalolin sauyin yanayi na daya daga cikin batutuwan da za su fi daukar hankali yayi taron yanayi na COP27 da Majalisar Dinkin Duniya za ta jagoranta daga ranar Lahadi mai zuwa a kasar Masar.

Wata kididdiga ta nuna cewar, kasashe masu arziki sun gaza cika alkawarin bayar da tallafin dala biliyan 100 da suka yi alkawarin mikawa kasashe masu tasowa a duk shekara, domin kuwa dala biliyan 83 kawai kasashen masu kumbar susa suka bayar a shekarar 2020.

A makon da ya gabata Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa ababu alamun hukumomin kasa da kasa sun kusa cimma burin rage kaifin dumamar yanayi zuwa kasa da maki 1.5 a ma'aunin Celsius, kamar yadda aka cimma yarjejeniyar yayin taron duniya kan matsalar sauyin yanayi a birnin Paris a shekarar 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.