Isa ga babban shafi

Sauyin yanayi: Duniya na bukatar dasa itatuwa a kadada sama da biliyan 2

Akwai bukatar duniya ta kebe wani yanki da ya fi Amurka girma domin dashen itatuwa da sauran matakan da za a dauka don cika alkawuran yaki da dumamar yanayi, a cewar wani bincike da ya yi gargadi a kan rashin tabbas game da takaita amfani da gurbatacciyar iska.

Wata mata da wani yaro suna tafiya a kan kogin da ya kafe na Zayandeh Roud wanda ke kasan gadar Si-o-seh Pol mai shekaru 400. A kasar Iran.
Wata mata da wani yaro suna tafiya a kan kogin da ya kafe na Zayandeh Roud wanda ke kasan gadar Si-o-seh Pol mai shekaru 400. A kasar Iran. AP - Vahid Salemi
Talla

Kusan kasashe 200 ne za su fara tattaunawa kan sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Masar daga ranar 6 ga watan Nuwamba, yayin da ake samun karuwar barnar ambaliyar ruwa, da tsananin zafi da kuma fari a duniya.

Kididdigar Majalisar Dinkin Duniya na baya-bayan nan ta nuna cewa manufofi da tsare-tsare na yanzu ba za su isa su takaita dumamar yanayi ko kuma kaucewa illolin yanayi ba.

Sabon binciken ya nuna cewa dole ne a sauya fasalin tsare-tsaren cimma yarjejeniyar sauyin yanayi, kamar dashen itatuwa don magance gurbacewar muhalli.

Wani rahoto kan tsare-tsaren daga kasashe 166 da Tarayyar Turai, da Jami’ar Melbourne ta fitar, an kiyasta cewa jimillar yankin da ake so na fili wajen dasa itatuwa, ana bukatar ya kai kusan hekta biliyan 1.2, kwatankwacin kadada biliyan 2.9, wanda hakan ke nufin ya fi girma Amurka, ko kuma ninki hudunsa na girman kasar Indiya.

Binciken ya yi nazari kan manufofin kasashe, musamman alkawurran da aka dauka na dogon lokaci, wanda ba a fito karara an bayyana adadin fadin kasar da ake bukata ba, sai dai an yi lissafin ne ta hanyar amfani da bayanai game da nau'ikan ayyuka da kuma cire bayanan amfani da sinadarin carbon daga nazarce-nazarcen kwararrun yanayi na Majalisar Dinkin Duniya.

Masanan dai sun gano cewa yayin da aka ware sama da hekta 550 don gyara gurbatacciyar kasa da kuma kare dazuka, an kiyasta kadada miliyan 630 don shirin kawar da gurbatacciyar iska da ke haddasa tsananin zafi da ambaliyar ruwa da fari, matakin da ya kamata kasashen duniya a halin yanzu su yi gaggawar dauka shine, dashen itatuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.