Isa ga babban shafi

Rasha ta koma yarjejeniyar fitar da hatsi daga Ukraine kwana 4 bayan ficewa

Jiragen ruwa sun ci gaba da aikin fitar da hatsi daga Ukraine yau laraba, bayan Rasha ta sanar da komawa cikin yarjejeniyar da ta kulla da Majalisar Dinkin Duniya wadda ke bayar da damar fitar da hatsin ga kasashen Duniya.

Wani jirgin dakon hatsi daga tashar jiragen ruwa ta Odessa.
Wani jirgin dakon hatsi daga tashar jiragen ruwa ta Odessa. AP - David Goldman
Talla

Kwanaki 4 bayan matakin Rashan na ficewa daga yarjejeniyar fitar da hatsin ne ma’ai’akatar tsaron kasar ta sanar komawa don ci gaba da aikin fitar da hatsin ga kasashen Duniya.

Gabanin matakin na Rasha dai akwai fargabar yiwuwar sake tashin farashin kayaki da kuma karancin abinci wanda yakin na Moscow a Ukraine ya haddasa.

Shugaba Recep Tayyib Erdogan wanda kasar sa ce ta shige gaba wajen kaiwa ga kulla yarjejeniyar tsakanin Rasha da Majalisar Dinkin Duniya a watan Yulin da ya gabata, ya shaidawa zaman majalisar kasar cewa da misalin karfe 12 na ranar yau jiragen sun ci gaba da aikin dakon kayakin abincin bayan shiga tsakani.

Ma’aikatar tsaron ta Rasha ta ce, sun amince da komawa cikin yarjejeniyar bayan samun tabbaci daga Ukraine game da tsaron jami’ansu wadanda ke aikin rakiyar jiragen dakon kayakin abincin.

Ma’aikatar wadda a baya ta yi zargin dakarun Ukraine da yiwa jami’anta da ke rakiyar jiragen kofar rago tare da farmakarsu a bakin aiki, ta ce yanzu ta samu tabbacin bayar da cikakken tsaro ga jami’an nata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.