Shugaba Xi Jinping na kan hanyar sake samun sabon wa’addin shugabancin China
Shugaban kasar Sin Xi Jinping a yau Lahadi ya yaba da manufofin jam'iyyarsa ta kwaminisanci wajen yaki da cutar Covid-19 yayin da yake bude taron shekara biyar na jam’iyyar inda dubban wakilai suka `halara da kuma niyar sake ba shi wa'adi na uku a shugabancin kasar ta China.
Wallafawa ranar:
A jawabinsa ya yaba da manufofin jam'iyyarsa ta kwaminisanci yayin da yake bude taron shekara biyar na jam’iyyar inda dubban wakilai suka `halara da kuma niyar sake ba shi wa'addi na uku a shugabancin kasar ta China.
A cikin jawabin bude taron da ya dauki tsawon sa’o’I daya da rabi, shugaba Xi ya daukaka da kuma kare tsare-tsare a karkashin mulkinsa.
Shugaba Xi ya jaddada cewa zai ci gaba da kokarin da jam'iyyar ke yi na kawar da cutar ta Covid, wanda ke kawo cikas ga rayuwar jama'a da kuma kawo cikas ga tattalin arzikin kasar.
Shugaban na China ya ce yakin da cin hanci da rashawa ya kawar da miyagun dabbi’u a cikin jam'iyyar gurguzu, da sojoji da kuma kasar ga baki daya.
Shugaba Xi ya kuma mayar da hankali kan batutuwan tsaro da ikon mallakar yankunan Hong Kong da kasar China ke ikirari mallaka a farkon jawabinsa.
Ya yaba da sauyin da Hong Kong ta yi tare da bin doka da oda.
Ya yi alkawarin da cewa ba zai taba yin watsi da amfani da karfi ba a tsibirin Taiwan mai cin gashin kan sa,al’amarin da ya janyo cece-kuce.
A cikin jawabi Shugaba Xi ya fi mayar da hankali kan al'amuran cikin gida, Xi ya shaidawa mahalarta taron cewa, kasar Sin za ta taka rawar gani sosai a harkokin tafiyar da harkokin duniya kan sauyin yanayi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu