Isa ga babban shafi

MDD ta yi watsi da shirin muhawara kan zargin cin zarafin ‘yan kabilar Uyghur a China

Hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta kada kuri'ar da ta yi watsi da shirin tafka muhawara kan zargin karuwar cin zarafin tsirarun kabilu a China ciki har da musulmi 'yan kabilar Uyghur da ke yankin Xinjiang, bayan da China ta bukaci hakan a wani abu mai kama da koma baya ga bukatun kasashen yamma.

Tsirarun musulmi 'yan kabilar Uyghur na rayuwa cikin kunci da wahala saboda takura da ta ke hakkin da su ke fuskanta daga gwamnatin Rasha.
Tsirarun musulmi 'yan kabilar Uyghur na rayuwa cikin kunci da wahala saboda takura da ta ke hakkin da su ke fuskanta daga gwamnatin Rasha. © Wikipedia
Talla

Amurka da kawayen ta a makon da ya gabata sun gabatarwa Majalisar wani daftari da ya kunshi bukatar gabatar da tafka muhawara kan gudanar da bincike game da zargin China da cin zarafin tsirarun kabilun.

Matakin Majalisar a jiya alhamis na zuwa ne bayan da shugabar hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya Michelle Bachelet ta gabatar da rahoton binciken da aka dade ana jira.

Rahoton dai ya kunshi yiwuwar aikata laifukan cin zarafin dan adam da azabtarwa musamman kan musulmi ‘yan kabilar Uyghur, da sauran musulmi da ke kananan kabilu.

Kasashen Turai dai sun jima suna jiran fitar wannan rahoto don fara bincike da kuma shirye-shiryen hukunta China kan laifin da ta aikata, don hana wata kasa aikata makamancin laifin na ta.

A zaman da hukumar ta yi a yau, mambobin ta 47 guda 19 sun kada kuri’ar amincewa da dakatar da tafka muhawarar yayin da 11 ke bukatar a gudanar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.