Isa ga babban shafi

An kammala taron MDD ba tare da cimma yarjejeniyar kare muhalli ba

An kammala taron Majalisar Dinkin Duniya na tsawon makwanni 2 ba tare da cimma jituwar da za ta kai ga kulla yarjejeniyar bai wa muhalli, tsirrai da kuma halittun cikin ruwa kariya ba.

Matsalar yanayi na ci gaba da zama babbar matsala a Duniya.
Matsalar yanayi na ci gaba da zama babbar matsala a Duniya. AP - Leo Correa
Talla

Manufar taron wanda aka karkare a daren jiya juma’a shi ne samar da mafita ga barazanar da ke tunkaro muhalli da tattalin arzikin Duniya, wanda masana ke ci gaba da gargadin cewa matsalar na kokarin kaiwa matakin da ba za a iya magancewa ba.

Bayan shekaru 15 ana gudanar da makamantan taron har sau 4  mahalarta taron har zuwa yanzu an gaza kulla halastacciyar yarjejeniyar da za ta kai ga magance matsalolin da tekuna duniya ke fuskanta da tuni aka fara ganin illarsu.

Jakadiyar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman kan abubuwan da suka shafi teku da dokokin kasa da kasa kan iyakar ruwa, Mrs Rena Lee da ta jagoranci zaman taron na makwanni 2 ta ce duk da cewa basu cimma wata matsaya ta azo a gani ba amma sun dan samu ci gaba idan an kwatanta da tarukan baya.

A cewar jami’ar yanzu ya ragewa babban zauren Majalisar sanya lokacin da taro karo na 5 zai gudana don sanin abin da za a cimma da mahukuntan kasashe.

An dai yi fatan taron na wannan karo da aka faro ranar 15 ga watan Agustan da muke ciki ya kai ga cimma yarjejeniyar baiwa muhallin kariya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.