Isa ga babban shafi

Dumamar yanayi ta haddasa tashin gobarar daji a sassan Turai

Faransa ta fuskanci matsanancin yanayin zafi a jiya Laraba, inda wasu daga cikin yankunanta ke gaf da  fuskantar tsananin zafin da ya riga ya mamaye yankuna da dama a kasashen Spain da Portugal, yayin da gobarar daji ta lalata manyan dazuzzukan yammacin Turai.

Wannan hoton da hukumar kashe gobara ta yankin Gironde ta bayar, ya nuna yadda wata gobarar daji da ta tashi a kusa da birnin Landiras da ke kudu maso yammacin Faransa ke barna, a ranar Laraba 13 ga Yuli, 2022.
Wannan hoton da hukumar kashe gobara ta yankin Gironde ta bayar, ya nuna yadda wata gobarar daji da ta tashi a kusa da birnin Landiras da ke kudu maso yammacin Faransa ke barna, a ranar Laraba 13 ga Yuli, 2022. AP
Talla

Wani jirgi mai saukar Angulu na masu aikin kashe wutar dajin da ta tashi a wasu sassan kasashen Turai ya fadi a gabar tekun kasar Girka, dai-dai lokacin da yake kokarin aikin kashe gobarar.

Bayanan da kafafen yada labaran cikin gidan kasar Girka suka fitar, na nuni da cewa an yi nasarar ceto mutane 2 cikin guda 4 da jirgin ya fadi da su, kuma ana ci gaba da aikin neman sauran mutane biyu.

Wani kwararre kan harkokin yaki da annoba na kasar, ya ce jirgin mai saukar Angulu ya doshi dajin Samos don tarar da takwarorinsa da ke kokarin kashe wutar dajin da ta tashi a yankin.

Bayanai na cewa wutar ta tashi a kasar ne da Misalin Karfe 11 na safiyar ranar Laraba agogon kasar, kuma tuni aka aike da jirage masu saukar Angulu guda uku da kuma masu aikin kashe gobara guda 50 don shawo kanta.

Kakkarfar guguwa na barazanar maida hannun agogo baya

To sai dai kuma wata kakkarfar guguwa da ke kara rura wutar, na zama barazana ga aikin masu kashe gobarar, yayin da kasashen Turai ke ci gaba da fama da tsananin zafi da ya zarta ma’aunin Celcius 30.

Gobarar daji na ci gaba da ruruwa a sassan Turai, inda ma'aikatan kashe gobara ke fafatawa da gobara a Portugal da Spain da kuma kudancin kasar Faransa.

A ranar Laraba Faransa ta fuskanci yanayi mai zafi da ba a saba gani ba, wanda hukumomi ke dangantawa da sauyin yanayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.