Isa ga babban shafi

Duniya na bikin ranar Hausa, harshe mafi yawan masu amfani da shi a Afrika

Miliyoyin Hausawa ne ke bikin wannan rana a kowacce 26 ga watan Agusta don tuni da kuma duba irin gagarumar gudunmawar da harshen na Hausa mafi girma a nahiyar Afrika ke bayarwa, inda a wannan karon bikin ke gudana hatta a kasashen da ke da karancin masu amfani da wannan harshe.

Harshen Hausa na ci gaba da yaduwa a sassan Duniya.
Harshen Hausa na ci gaba da yaduwa a sassan Duniya. Pinterest
Talla

Kasashen Najeriya da Nijar da kamaru da Chadi baya ga Ghana da Burkina Faso na matsayin 'yan gaba gaba da ke gudanar da bikin wannan rana la'akari da yadda yaren ke da matukar tasiri a kasashen.

Ranar wadda yau ne karo na 8 da ake gudanar da bikinta na da nufin hada kan Hausawa baya ga samar da ci gaba mai dorewa dama bunkasa harshen ba kadai a yankunan da ke da rinjayen Hausawa ba har ma a yankunan da ake da karanci masu amfani da wannan harshe.

Hausa da ke matsayin harshe mafi karfi a nahiyar Afrika galibin kasashen yammacin nahiyar ke amfani da shi da kaso mai yawa a Najeriya, kuma harshen na daga cikin yaruka masu saurin yaduwa a nahiyar Afrika dama wasu sassa na duniya ta yadda harshen ke yin awon gaba da kananun yarukan da ke makwabtaka da Hausawa.

Kawo yanzu dai babu sahihin bayani kan asali ko kuma lokacin da aka fara amfani da harshen Hausa a ban kasa, amma batutuwa da dama na alakanta saurin yaduwarsa da fataucin da aka san Bahaushe da yi zuwa sassan duniya, kafin daga bisani kafofin yada labarai su sake bunkasa harshen.

Harshen Swahili da ke da alaka da larabci ya shiga gaban Hausa ne kasancewarsa wanda ake amfani da shi a hukumance kama daga makarantu da sauran muhimman gurare musamman a kasashen kudanci da gabashin Afrika sai dai Hausa ta zarta shi yawan jama'ar da ke amfani da harshen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.