Isa ga babban shafi

Isra’ila ta sha alwashin shafe mako guda ta na luguden wuta a Gaza

Ma’aikatar tsaron Isra’ila ta yi barazanar ci gaba da luguden wuta a yankin Gaza har zuwa nan da mako guda don kame ‘yan ta’addan yankin Falasdinu dai dai lokacin da aka shiga rana ta biyu Sojinta na barin wuta a wani yanayi da rikicin bangarorin biyu ya tsananta tun bayan yakin bara.

Wani yanki na Gaza da Isra'ila ke yiwa luguden wuta.
Wani yanki na Gaza da Isra'ila ke yiwa luguden wuta. AP - Abdel Kareem Hana
Talla

Bayanan da Isra’ila ta fitar ta ce dole ce ta sanya ta kaddamar da hare-haren don kakkabe ‘yan ta’addan da ke kitsa kai mata farmaki biyo bayan rikicin baya-bayan nan a kan iyakarta da yankin na Gaza da ke Falasdinu.

Kakakin Sojin Isra’ila ya bayyanawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa dakarunsu a shirye su ke su ci gaba da kai farmakin har zuwa nan da mako guda.

Tuni dai kasashe da Rasha akan gaba suka fara kiraye-kirayen dakatar da farmakin na Isra'ila a Gaza, yayinda Tarayyar Turai ta bukaci kai zuciya nesa tsakanin bangarorin biyu bayan da ya kashe tarin fararen hula ciki har da kankanuwar yarinya ‘yar shekaru 13.

Ma’aikatar lafiyar yankin na Gaza da Hamas ke jagoranci ta ce hare-haren na Isra’ila ya kashe mutane 13 tare da jikkata wasu 110 yayinda daruruwan iyalai suka rasa matsugunansu.

Tun bayan yakin kwanaki 11 da ya barke tsakanin bangarorin biyu a watan Mayun 2021 ba a sake samun barkewar kakkarfan rikici da manyan makamai tsakaninsu ba inda bayana hare-haren yau asabar da Isra’ilan ta kai da makaman roka, fargaba ta tsannata kan yiwuwar juyowar makamancin yakin na bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.