Isa ga babban shafi

Isra'ila ta kai farmaki kan cibiyoyin Hamas a Gaza

Jiragen yakin Isra'ila sun kai hari kan wasu cibiyoyin kera makaman sojojin Hamas dake Zirin Gaza a jiya Asabar, abinda rundunar sojin Isra’ilan ta bayyana a matsayin ramuwar gayya kan harba makamin roka cikin kasar daga yankin Falasdinu.

Wasu jiragen yakin Isra'ila.
Wasu jiragen yakin Isra'ila. REUTERS/Amir Cohen
Talla

Sanarwar ta ce,  farmakin kan Gaza ya zo ne bayan da Hamas ta harba makamin roka kan fararen hular Isra'ila a kudancin kasar.

A ranar Asabar ne kuma, Isra'ila ta ce ta dakatar da baiwa karin ma’aikatan Falasdinawa izinin shiga cikinta daga yankin Gaza saboda harba mata makamin na roka da mayakan falasdinun suka yi.

Akalla Falasdinawa 12 suka jikkata a harin da sojojin Isra'ila suka kai a ranar Juma'a a Jenin, dake zama tungar kungiyoyi masu dauke da makamai a yammacin gabar kogin Jordan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.