Isa ga babban shafi

Yau take Sallah Babba ga al'ummar Musulmi a sassan duniya

Yau Asabar 10 ga watan Zul Hijja shekara ta 1443 bayan hijirar Annabi Muhd (SAW) daga Makka zuwa Birnin Madina, al’ummar Musulmi ke murnar ranar Sallar layya a sassan duniya, daya daga cikin muhimman ranekun ibada a addinin Islama.

Shugaban kasar Syria Bashar Assad yayin gabatar da Sallar Idi a birnin Aleppo, inda yakin basasar kasar da ya shafe shekaru fiye da 10 ya fara barkewa.
Shugaban kasar Syria Bashar Assad yayin gabatar da Sallar Idi a birnin Aleppo, inda yakin basasar kasar da ya shafe shekaru fiye da 10 ya fara barkewa. AP
Talla

Yanka dabbobin layya ga wadanda suka samu dama, bayan halartar Sallar Idi, na daga cikin abubuwa mafi muhimmanci a wannan rana.

A jiya Juma’a, mahajjata dake kasar Saudiyya, suka gudanar da tsayuwar Arafa, yayin da kuma wadanda basu samu zuwa ba, suka gudanar da ibadar azumtar ranar daga gida.

Idan aka dauke batun tattalin arziki, za a iya cewa akwai sassauci yayin Sallar layya ta bana, la’akari da yadda tuni hukumomi a sassan duniya suka sassauta dokokin hana walwala, wadanda a baya ke aiki saboda barkewar annobar Korona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.