Isa ga babban shafi
Duniya

Musulmi na murnar Sallar layya karkashin matakan dakile annobar coronavirus

Yau Juma’a 10 ga watan Dhul Hijja take ranar Sallar layya ga al’ummar Musulmi a sassan duniya, lokacin da ake gudanar da muhimmiyar ibadar yanka ko soke dabbobi, kama daga Shanu, tumaki da rakuma.

Wani matashi a kasuwar dabbobi dake kauyen Al Manashi a yankin Giza dake Masar, yayin cinikin dabbar layya.
Wani matashi a kasuwar dabbobi dake kauyen Al Manashi a yankin Giza dake Masar, yayin cinikin dabbar layya. REUTERS/Mohamed Abd El Ghany
Talla

Kamar Sallar Azumin bana, wannan Sallar layyan ma ta zo ne cikin halin fama da annobar COVID-19, wadda ake fargabar sake barkewarta a karo na 2, bayan saukin da ta yi a baya.

Wannan yanayi ne ya sanya gwamnatocin kasashen duniya musamman a nahiyar Afrika, daukar matakan soke halartar Sallar idi da kuma hana bukukuwa, yayinda kuma wasu hukumomin gudanar da bukukuwan kawai suka soke, inda suka bada damar yin Sallar Idi.

A Saudiya, ranar Alhamis Mahajjata suka yi hawan Arafa da ke zama babban rukunin aikin hajji, inda aka tanadi cikakken tsaro duk da cewa tsirarun mutane ke gudanar da aikin hajjin bana saboda annobar coronavirus.

Karon farko a tarihin baya-bayan nan, tsirarun mutane ne da adadinsu bai wuce dubu 10 ba ke gudanar da aikin hajjin bana, sabanin shekarun da suka gabata da ake samun kimanin Mahajjata miliyan biyu da doriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.