Isa ga babban shafi

Kasashe 200 sun kulla yarjejeniyar bai wa halittu kariya daga gushewa

Bayan shafe mako guda Majalisar Dinkin Duniya na jagoranci taron yaki da dumamar yanayi a birnin Nairobin kasar Kenya, wakilan kasashe 200 da suka halarci zaman, sun cimma matsaya wajen kulla yarjejeniyar da za ta bai wa tsirrai da halittu kariya daga barnar dan adam a ban kasa.

Wasu nau'ikan halittu da ke kokarin bacewa a ban kasa.
Wasu nau'ikan halittu da ke kokarin bacewa a ban kasa. Murali Krishnan
Talla

Taron na tsawon mako guda da aka karkare a jiya lahadi tsakanin kasashe 196 mambobin kwamitin yaki ko kuma bai wa halittu da tsirrai kariya na Majalisar Dinkin Duniya, na zuwa ne watanni 6 gabanin babban taron yanayi na COP15 da Majalisar ke shirin gudanarwa cikin watan Disamba.

Manufar wannan yarjejeniya da kasashen kusan 200 suka kulla a Nairobin Kenya shi ne bai wa muhalli da halittun da ke rayuwa cikinsa cikakkiyar kariya daga ta’annatin bil’adama da nufin samar da wani daftari da zai zayyano yadda za a samar da yanayi da bazai cutar da dan adam ba nan da shekarar 2050 bayan cimma muhimman tsare-tsaren a 2030.

Akwai dai yakinin cewa matukar aka cimma muhimman tsare-tsaren wannan yarjejeniya a 2030 za ta yi kamanceceniya da yarjejeniyar Paris sai dai banbancin guda a mai kare halittun ban kasa guda kuma a mai kare gurbacewar muhalli ko dumamar yanayi.

Sai dai masana na ganin matsayar da aka cimma a taron na Kenya ba ta kai yanayin da za ta samar da gagarumin ci gaba a kokarin bai wa halittun da muhalli kariya ba.

Daraktan gangamin bai wa halittun kariya na Majalisar Dinkin Duniya Brian O’Donnell ya ce muhimman batutuwa da ya kamata a kammala cimma yarjejeniya akansu yayin taron na Kenya a dage su zuwa haduwa a taron watan Disamba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.