Isa ga babban shafi

Fafaroma ya jinkirta kai ziyara a Afirka saboda rashin lafiya

Shugaban mujami’ar Katolika na duniya Fafaroma Francis, ya jinkirta kai ziyara a wasu kasashen Afirka saboda yana fama da ciwo a gwiwarsa kamar dai yadda fadar Vaitican ta sanar.

Fafaroma Francis na gabatar da huduba daga dandalin Saint-Peters ,ranar 1 ga watan yunin 2022.
Fafaroma Francis na gabatar da huduba daga dandalin Saint-Peters ,ranar 1 ga watan yunin 2022. AFP - FILIPPO MONTEFORTE
Talla

Sanarwar dai ta ce an jinkirta wannan rangadi da ya kamata Fafaroma ya kai a jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo da Sudan ta Kudu ne bisa shawarar likitocinsa.

Da farko dai an tsara ce jagoran na mujami’ar Katolika zai gudanar da ziyarar ce daga ranar 2 zuwa 7 ga watan Yulin wannan shekara, to sai dai kawo yanzu ba a bayyana sabuwar ranar da zai gudanar da wannan ziyara ba.

Francis, mai shekaru 85 a duniya, yana fama da ciwo mai radadi a gwiwarsa ta kafar dama, inda a cikin watan jiya ma ya bayyana gaban masu ibada a kan keken guragu.

Kafin nan, Fafaroma ya soke kai ziyara saura da dama a wasu kasashen, da suka hada har da Libanan a wannan wata na y

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.