Isa ga babban shafi
Vatican

Paparoma ya gana da limamin Azhar a Vatican

Shugaban darikar mabiya katolika ta duniya Paparoma Francis ya gana da babban limamin jami’ar Azhar da ke birnin Alkahira na Masar, Sheik Ahmad Tayeb, lamarin da ake  kallo a matsayin wani abu mai cike da tarihi, yayin da jagororin biyu suka rungumi juna tare da sumbatar kan su bayan kammala tattaunawa a fadar Vatican.

Shugaban mabiya darikar Katolikan na Duniya Paparoma Francis da babban limamin jami'ar Azhar ta Masar
Shugaban mabiya darikar Katolikan na Duniya Paparoma Francis da babban limamin jami'ar Azhar ta Masar s.yimg.com
Talla

Ganawar wadda aka shafe tsawon mintina 30 ana yin ta a yau, ta karkare cikin inganta hulda tsakanin Islama da Kirista da ake kallo a matsayin manyan addinai guda biyu a duniya.

Mai magana da yawun Vatican ya ce, har ila yau, shugabannin sun tattaunawa kan kalubalen da hukumomi da mabiya addinan biyu ke fuskanta.

Kana za su yi aiki tare wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya tare da kyamar ayyukan ta’addanci da rikice rikice musamman a yankin gabas ta tsakiya.

A cewar Sheik Tayeb, ya amsa gayyatar Paparoma Francis ne domin amfani da wata dama ta yada zaman lafiya da kyakkyawar zamantakewa.

A can baya dai an samu tsamin dangantaka tsakanin fadar ta Vatican da mabiya Islama saboda kalaman da Paparoma Benedict na wancan lokacin ya yi a shekarar 2006, inda aka fahimci cewa yana alakanta tashe tashen hankula da musulunci, abinda ya haifar da zanga zanga a wasu kasashen duniya.

Kazalika a shekara ta 2000 ne, Paparoma John Paul na II ya gana da Shehun Azhar na wancan lokacin a birnin Alkahira, kuma hakan ya faru ne gabanin harin ranar 11 ga watan Satumba shekarar 2001 wanda kungiyar Al-Qaeda ta kai birnin New York na Amurka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.