Isa ga babban shafi
Corona-Duniya

Corona ta kashe mutane miliyan 2 a Turai wasu miliyan guda a Amurka- WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon harbuwa da cutar korona a nahiyar Turai ya zarce miliyan 2, yayinda fadar gwamnatin Amurka ke cewa 'yan kasar sama da miliyan guda suka mutu sakamakon annobar.

Corona ta shiga sahun cutuka mafiya lakume rayuka da aka taba gani a tarihi.
Corona ta shiga sahun cutuka mafiya lakume rayuka da aka taba gani a tarihi. © via REUTERS - Social Media
Talla

Sanarwar da Hukumar ta fitar yau na kunshe da adadin mutane sama da mutum miliyan biyu da suka sheka lahira sakamakon harbuwa da cutar a kasashe 53 daka Turai da wasu kasashen Asia.

Alkaluman da Hukumar ta gabatar sun nuna cewar ya zuwa yau laraba mutane miliyan 2 da dubu 2 da 58 suka mutu a yankin daga cikin sama da miliyan 218 da suka harbu da cutar.

Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da Amurka, kasar da aka fi samun wadanda suka harbu da cutar a duniya tace yawan mutanen da cutar ta kashe a kasar ta sun zarce miliyan guda.

Bayan sama da shekaru 2 da barkewar cutar a duniya, kasashen Turai da dama sun bayyana shirin watsi da matakan da suke dauka na dakile yaduwar cutar musamman abinda ya shafi zirga zirga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.