Isa ga babban shafi
Hollywood-Smith

Will Smith ya shararawa mai gabatarwa mari yayinda ake bashi kyautar Oscar

Tauraron finafinan Hollywood da ke Amurka Will Smith ya lashe kyautar gwarzon jarumi na bana da yafi kowa nuna bajinta a matsayin acta, saboda rawar da ya taka a matsayin mahaifin fitattun 'yan wasan tennis na duniya Venus da Serena Williams a wani sabom fim da King Richard.

Will Smith lokacin da ya ke shararawa mai gabatarwa Chris Rock mari bayan mika masa kyautar Oscar.
Will Smith lokacin da ya ke shararawa mai gabatarwa Chris Rock mari bayan mika masa kyautar Oscar. REUTERS - BRIAN SNYDER
Talla

Sai dai Smith ya yi abin ba za ta a wajen bikin, inda ya je ya shararawa mai gabatar da shirye shirye Chris Rock mari saboda abinda ya kira shaguben da ya yiwa iyalin sa.

Will Smith gwarzon jarumi na bana da ya lashe kyautar Oscar da film dinsa na CODA.
Will Smith gwarzon jarumi na bana da ya lashe kyautar Oscar da film dinsa na CODA. Chris Pizzello/Invision/AP - Chris Pizzello

Smith ya yi nasara ne da film dinsa mai suna Coda, wanda ya karkata ga barkwanci, wanda ke matsayin karon farko da jarumin ya lashe irin wannan kyauta duk da rawar ganinsa a manya fina-finai da suka fito da sunansa irinsu Bad Boys da Independence Day da kuma Men In Black cikin fiye da shekaru 30 da ya shafe a masana'antar.

Daga cikin wadanda suka lashe lambar girma a wajen bikin da akayi a birnin Los Angeles akwai Jane Campion a matsayin Daraktan da yafi fice da Jessica Chastain a matsayin tauraruwar da tafi fice, sai kuma Troy Kotsur a matsayin mai taimakawa tauraro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.