Isa ga babban shafi
Fina-Finai

'Yar China ta kafa tarihin lashe kyautar Oscar

Fim din Nomadland da ke nuna yanayin rayuwar tsofaffin Amurkawa masu gararamba a cikin kwarababbiyar motar akori-kura, ya lashe lambar yabo ta Oscar saboda kyawun daukar hotonsa.

Chloé Zhao wadda ta bada umarni a fim din Nomadland
Chloé Zhao wadda ta bada umarni a fim din Nomadland Chris Pizzello POOL/AFP
Talla

Chloe Zhao wadda ta bada umarni a wasan kwaikwayon na Nomadland, ta kafa tarihin zama mace ta farko wadda ba baturiya ba da aka karrama da lambar yabo ta Oscar.

Kazalika ta zama mace ta biyu a tarihi  da ta lashe kyautar a matsayinta ta mai bada umarni bayan Kathryn Bigelow wadda ta fara bude babin irin wannan tarihin a shekaarr 2010, lokacin da aka karrama ta saboda fim din “The Hurt Locker.”

Zhao ‘yar asalin China ce, amma kafafen yada labarai na kasarta ba su yada labarin nasararta ba.

A can baya, Zhao ta taba janyo cece-kuce a China saboda yadda ta caccaki kasarta a wata hira da ta yi da manema labarai.

A bangare guda, Frances McDormand ita ma ta samu lambar yabo ta gwarzuwar jaruma, yayin da Anthony Hopkins ya lashe kyautar a matsayinsa na gwarzon jarumi.

Hopkins mai shekaru 83, ya zama jarumin fina-finai mafi tsufa a tarihi da ya lashe kyautar ta Oscar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.