Isa ga babban shafi
Ukraine - Rasha

Zelensky ya bukaci tattaunawar gaggawa yayin da Rasha ta zafafa hare-hare

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky, ya yi wani sabon kira na neman zaman lafiya mai ma'ana da Moscow, yayin da Rasha ta ce sojojinta sun shiga tsakiyar birnin Mariupol dake kusa da tashar jiragen ruwa da ta yi wa kawanya.

Jami'an kashe gobara na kasar Ukraine sun kashe gobarar da ta tashi a wani dakin ajiyar kaya bayan wani harin bam a birnin Kyiv na kasar Ukraine Alhamis 17 ga Maris, 2022.
Jami'an kashe gobara na kasar Ukraine sun kashe gobarar da ta tashi a wani dakin ajiyar kaya bayan wani harin bam a birnin Kyiv na kasar Ukraine Alhamis 17 ga Maris, 2022. AP - Vadim Ghirda
Talla

Cikin wani sabon faifan bidiyo da aka watsa da shafin Facebook wannan Asabar, Volodymyr Zelensky ya bukaci tattaunawar gaskiya da Rasha Asabar, yace idan ba’a samu wannan damar ba to Allah kadai yasan irin asarar da kasar zatayi, wanda zatayi wuyan farfadowa.

Hanyoyin jinkai

• Ukraine na fatan bude hanyoyin jin kai 10 a ranar Asabar don kwashe 'yan kasar, a cewar mataimakin firaministan kasar Iryna Vereshchuk.

• Dakarun Rasha da ke samun goyon bayan mayakan Checheniya sun kutsa kai cikin kariyar birnin Mariupol da aka yi wa kawanya, kuma a halin yanzu suna cikin birnin, wanda ke fama da hare-haren Rasha cikin ‘yan kwanaki.

Makami mai linzami

• Sojojin Rasha sun ce sun yi amfani da makami mai linzami kirar Kinzhal a karon farko a yakin da suke yi a Ukraine. Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta fada a ranar Asabar cewa "makamai masu linzami na sararin samaniya sun lalata wani babban dakin ajiyar karkashin kasa mai dauke da makamai masu linzami da jiragen sama" a kauyen Deliatyn na yankin Ivano-Frankivsk.

• Wata jami'ar kare hakkin bil'adama ta Ukraine Lyudmyla Denisova ta fada a ranar Juma'a cewa mutane 130 ne aka ceto cikin gine-gine da ke Mariupol bayan wani hari da jiragen saman Rasha suka kai, inda daruruwan mutane suka nemi mafaka.

 Masu aikin ceto na ci gaba da neman wadanda ke da sauran nunfashi.

• Hukumomin birnin Kyiv a ranar Juma'a sun ce mutane 222 ne aka kashe a babban birnin kasar tun lokacin da Rasha ta mamaye Ukraine.

'Yan gudun hijira

• Hukumar UNHCR ta ce sama da 'yan Ukraine miliyan 3.25 ne suka yi gudun hijira a kan iyaka tun lokacin da aka fara yakin a ranar 24 ga Fabrairu, inda sama da miliyan 2 suka tsallaka kan iyakar Poland. Hukumar kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan rabin wadanda suka gudu yara ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.