Isa ga babban shafi
Rasha - Ukraine

Rasha ta yi amfani da makamin da gudunsa ya ninka sauti sau 10 a Ukraine

Ma’aikatar tsaron Rasha ta  ce ta yi amfani da sabon makami mai linzami mai matsanancin gudu a karon farko wajen lalata rumbunan makaman Ukraine.

 Vladimir Putin, shugaban Rasha.
Vladimir Putin, shugaban Rasha. AP - Alexei Nikolsky
Talla

Rasha ba ta taba yarda cewa t yi amfani da wannan makami mai linzami ba, kuma kamfanin dillancin labaran kasar ya ruwaito cewa wannan ne karo na farko da ta yi amfani da makamin da aka wa lakabi da Kinzhal a yammacin Ukraine.

Makami mai linzami na Kinzhal mai dankaren gudu, wanda aka kwatanta da gudun sauti ninki 10, ya lalata dimbim rumbunan makamai masu dauke da makamai masu linzami da alburushan harbo jiragen sama a kauyen Deliatyn, a yankin Ivano-Frankivsk.

Sai dai wani kakakin ma’ikatar tsaron Rasha ya kauce wa yin karin bayani a lokacin da kamfanin dillancin labaran Faransa ya tuntube shi.

Putin  ya yi bayani a kan Kinzhal

Shugaba Rasha Vladimir Putin ya bayyana makamin Kinzhal, mai linzami a matsayin makmin da ya dace da aikin da suke yi, wanda gudunsa ya ninka na sauti sau 10, kuma babu na’urar da za ta iya kakkabo shi.

Makamin na Kinzhal na daya daga cikin makaman da Putin ya baje kolinsu a yayin da ya gabatar da jawabi kan halin da kasar ke ciki a shekarar 2018.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.