Isa ga babban shafi
Ukraine-Rasha

Amurka ta bai wa Ukraine makaman yaki da Rasha

Shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da tallafin Dala biliyan 1 tare da aikewa da makamai masu cin dogon zango da kuma jirage marasa matuka ga Ukraine, yayin da ya jaddada kudirinsu na agaza wa kasar a yakin da take gwabzawa da Rasha.

Daga cikin makaman har da wadanda ke kakkabo jiragen sama
Daga cikin makaman har da wadanda ke kakkabo jiragen sama AP
Talla

Kudaden tallafin da Amurka ta bayar a daidai lokacin da sojojin Rasha ke gab da shiga babban birnin Kyiv, sun hada da Dala miliyan 200 da aka bayar a karshen mako da kuma Dala miliyan 800 da Majalisar Dokokin Amurka ta amince da shi a makon jiya.

A yayin sanar da tallafin, shugaba Biden ya ce, kai tsaye za su tura wa Ukraine kayayyakin soji daga Ma’aikatar Tsaron Amurka domin taimaka wa kasar wajen tunkarar Rasha da ta yi mata mamaya.

Kamar dai yadda aka yi zato, shugaban na Amurka bai mayar da hankali kan haramta wa Rasha ratsa sararin samaniyar kasashen yammaci ba, matakin da ita ma Kungiyar Tsaro ta NATO ta ki amincewa da shi saboda gudun kazancewar rikicin.

Ana ganin daukar wannan matakin na harmata wa Rasha ratsa sararin samaniyar,  ka iya tilasta wa kasashen NATO yin gaba-da-gaba da Rashar.

Fadar gwamnatin Amurka ta White House ta ce, Ukraine za ta karbi karin makaman kakkabo jiragen yaki har guda 800 da kuma makaman tarwatsa tankokin yaki guda dubu 900, ba ya ga wasu kananan makamai guda dubu 7 da kuma harsashen bindiga miliyan 20.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.