Isa ga babban shafi
Italia-Poland

Matteo Salvini na Italia ya gamu da kakkausar suka kan goyan bayan Putin

Magajin Garin Przemysl a Poland Wojciech Bakun ya caccaki Matteo Salvini na Italy kan wasu kalamansa da ke nuna goyon bayan shugaba Vladimir Putin na Rashaa mamayar da ya ke ci gaba da yiwa Ukraine.

Matteo Salvini, na jerin 'yan gaba gaba da ke goyon bayan shugaba Vladimir Putin.
Matteo Salvini, na jerin 'yan gaba gaba da ke goyon bayan shugaba Vladimir Putin. REUTERS/Alberto Lingria
Talla

Wani faifan bidiyo ya nuna yadda Bakun ya caccaki Salvini yayin ziyarar dubban ‘yan gudun hijirar da rikicin na Ukraine ya raba da matsugunansu a yammacin jiya talata.

Tsawon shekaru Salvini jagoran jam’iyyar League a Italiya na nuna goyon baya ga Putin na Rasha inda a lokuta da dama ake ganinsa sanye da riga mai dauke da hoton Putin a bangare guda kuma ya yi kaurin suna wajen kare manufofin jagoran a shafukan sada zumunta.

A ganawar ta Wojciech Bakun, da Salvini ya bukaci dan siyasar na Italiya ya yi dubi kan irin bannar da mutumin da ya kira abokinsa ke aikatawa nahiyar turai.

Mr Bakun ya ce tun bayan farowar yakin na kwanaki 14 a kowacce rana akan samu mutane dubu 50 da ke tsallaka iyaka.

Sai dai a martanin Salvini ya shaidawa Mr Bakun cewa babu sauran girmamawa tsakaninsu, kuma ya gode da kalamansa.

Mr salvini dai ya rika zagaya ‘yan gudun hijirar tare da basu hakuri cikin harshen ingilishi.

Wasu daga cikin ‘yan gudun hijirar sun rika mayar da martani ga Salvini da cewa ‘‘kana da cikakkiyar damar caccakar Putin a yanzu, yayinda wani daban ya kwarara kuwwar cewa bama bukatar tausayawarka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.