Isa ga babban shafi
Rasha - Ukraine

Hana shawagin jiragen sama a Ukraine zai jefa Turai cikin bala’i - Putin

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yi gargadin cewa duk kasar da ta nemi sanya dokar hana shawagin jirage a sararin samaniyar Ukraine, gwamnatinsa za ta dauke ta a matsayin wadda ta shiga yaki da ita kai tsaye.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin.
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin. © Sputnik/Aleksey Nikolskyi/Kremlin via REUTERS
Talla

Putin ya bayyana haka ne yayin ganawa da ma'aikatan kamfanin jiragen sama na kasar Aeroflot a yau Asabar, inda ya kara da cewa, sanya dokar hana zirga-zirgar jiragen sama a Ukraine zai haifar da "mummunan sakamako da bala'i ba ga Turai kadai ba har ma da duniya baki daya".

Wannan gargadi dai ya zo ne sa’o’I kalilan bayan da, kungiyar tsaro ta NATO ta yi watsi da bukatar Ukraine na hana zirga-zirgar jiragen sama a sararin samaniyarta, abinda ya janyo kakkausar suka daga shugaban kasar Volodymyr Zelenskyy, wanda ya ce matakin ya baiwa Rasha karin damar cigaba da yi wa kasarsa ruwan bama-bamai.

Sakatare Janar na NATO Jens Stoltenberg ne ya sanar da matakin kin amincewa da haramta zirga-zirgar jiragen sama a Ukraine, bayan wani taron gaggawa na kasashe 30 da ya jagoranta a Brussels.

Kawo yanzu kididdiga ta nuna cewar, fiye da ‘yan Ukraine miliyan 1 suka tsere daga kasar, kuma dubu 780,000 daga cikinsu sun tsallaka ne cikin Poland, tun bayan da Rasha ta fara mamaye kasarsu a ranar 24 ga watan Fabrairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.