Isa ga babban shafi
Rasha - Ukraine

Putin ya yi barazanar katse ci gaba da zaman Ukraine a matsayin kasa

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi barazanar katse ci gaba da kasancewar Ukraine a matsayin yantatar kasa, a yayin da mamayar da ya yi wa kasar ke ci gaba da gamuwa da turjiya, kuma tattalin arzikin kasarsa ke dada dankwafewa sakamakon takunkumai masu gauni.

FShugaban Rasha Vladimir putin.
FShugaban Rasha Vladimir putin. AP - Pavel Golovkin
Talla

Putin ya gargadi shugabancin Ukraine cewa idan suka ci gaba da abin da suke yi, tamkar suna jingine ci gaba da kasancewar kasar kenan, kuma idan hakan ya faru laifinsu ne.

Rasha ta ci gaba da kai hare hare Ukraine, amma shugaba Zelensky wanda ke turjewa ya ce dakarunsa na mayar da zazzafan martani a yankin Kharkiv, birni na biyu mafi girma  a kasar, kuma su ma maharan na dandana asarar da ko a mafarki ba su taba gani ba.

Shi ma ministan harkokin wajen Ukraine Dmytro Kuleba cewa yake, jini na kwarara daga Ukraine, amma sam, ba ta fadi ba, yana mai cewa asirin sojin Rasha da ke da karfin gaske ya tonu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.