Isa ga babban shafi
Canada - zanga-zanag

Masu zanga-zanga sun katse iyakar Canada da Amurka

Zanga-zangar kin jinin dokokin yaki da Corona masu tsauri da aka faro daga kasar Canada ta fara fantsama zuwa wasu kasashen Turai. Hakan dai na barazanar haifar da tashin hankali a kasashen, wadanda dama mutanen su sun jima suna nuna adawa da wasu dokokin.

Masu zanga zangar adawa da dokokin korona a kasar Canada 8/02/2022.
Masu zanga zangar adawa da dokokin korona a kasar Canada 8/02/2022. AP - Adrian Wyld
Talla

Tun da fari dai jama’ar Canada ne suka fara zanga-zangar kin jinin wasu dokokin yaki da Corona da suka ce masu tsauri ne ta hanyar jera manyan motocin daukar kaya da rufe hanyoyi da su.

Haka kuma mutanen sun rufe wasu daga cikin muhimman iyakokin kasar da wasu gadoji, wanda hakan ya fara shafar hada-hadar sufuri da kuma harkokin kasuwanci.

Brazil

A yanzu dai zanga-zangar ta fara nuna alamun fantsama zuwa wasu kasashen, don kuwa tuni jama’ar kasar Brazil suka sanar da gudanar da makamanciyar zanga-zangar a ranar Litinin, yayin da tuni na Faransa wadanda dama sun yi suna a gudanar da mummunar zanga-zanga suka sanar da ranar fara ta su.

Amurka

Baya ga wadannan, kasashen Amurka da New Zealand ma akwai alamun jama’ar kasar su dauki makamancin wannan matakin.

Tuni dai Prime ministan kasar Justin Trudeau ya gargadi al’umma game da kara ta’azzara zanga-zangar da kuma lalata kayan gwamnati, yana mai hango irin mummunan yanayin da kasar ka iya fadawa idan zanga-zangar ta wastu wasu kasashen a yanayin da ake ciki.

Faransa

'Yan sandan Faransa ma sun yi gargadin cewa za su hana wadanda ake kira "ayarin 'yanci" daga katse hanyoyi a birnin Paris, awani matakin shirin ko ta kwana kan taho-mu-gama da masu zanga-zanga da 'yan sandan suka yi wadda ta gurgunta birnin Ottawa na Canada.

A ranar Juma'a ne ake sa ran masu zanga-zanga cikin ayarin motocin daga sassa daban-daban na kasar Faransa su hallara a babban birnin kasar, domin adawa kan takunkumin hana yaduwar cutar korona da kuma tsadar rayuwa sakamakon hauhawar farashin makamashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.