Isa ga babban shafi
Faransa

Dubban Faransawa sun yi zanga-zangar adawa da sabuwar dokar yaki da Korona

Ma’aikatar cikin gidan Faransa ta ce, kimanin mutane dubu 38,000 ne suka yi zanga-zangar adawa da sabuwar dokar tilasta yin allurar rigakafin Korona, fadin kasar.

Masu zanga-zanga a birnin Paris.
Masu zanga-zanga a birnin Paris. AFP - CHRISTOPHE ARCHAMBAULT
Talla

A birnin Paris kadai, kididiga ta nuna cewar, kimanin mutane dubu 5 da 200 suka fita zanga-zangar a jiya Asabar, wadda ta samu halartar daruruwan masu goyon bayan, dan takarar shugaban kasa Florian Philippot mai dawa da EU.

Daga ranar Litinin 24 ga watan Janairu, ya zama dole wadanda shekarunsu suka kai 16 zuwa sama su nuna yin allurar rigakafin Korona kafin shiga gidajen abinci ko mashaya, da kuma wuraren shakatawa da sufuri.

A karshen makon da ya kare, Majalisar Tsarin Mulkin Faransa ta amince da sabuwar dokar yaki da Korona, wadda za ta tilastawa mutane masu shekaru 16 zuwa sama nuna shaidar yin allurar rigakafin cutar, kafin shiga wuraren taron jama'a.

Sabuwar dokar dakile yaduwar annobar ta Korona dai, wani bangare ne na yunkurin shugaba Emmanuel Macron da ya sha alwashin kuntatawa tsirarun mutanen da ba a yi musu allurar rigakafin cutar Koronar ba.

Dokar za ta maye gurbin nuna takardar shaidar gwajin mutum ba ya dauke da cutar Korona, ko kuma shaidar da ke nuna warkewa daga cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.