Isa ga babban shafi

An soma kauracewa zanga-zanga adawa da rigakafin Koronna

A Faransa,wasu alkaluma na dada nuni cewa an soma fuskantar karancin jama’a tarurrukan nuna adawa da matakin gwamnati na tilastawa jama’a nuna izini ko  sheidar nan dake tabbatar da cewa sun karbi allurar rigakafin cutar Covid 19 a wannan kasa.

Masu adawa da matakin Korona a Faransa
Masu adawa da matakin Korona a Faransa AFP - CHRISTOPHE ARCHAMBAULT
Talla

A wasu alkaluma daga ofishin Minitan cikin gidan kasar ta Faransa a duk ilahirin kasar mutane dubu 54 ne suka amsa kiran halartar ganggamin a maimakon  dubu 105 da suka fito a makon da ya gabata.

Hukumar dake yaki da cutar Koronna a Faransa
Hukumar dake yaki da cutar Koronna a Faransa ALAIN JOCARD AFP

A babban birnin kasar Paris a wurarre hudu daban a jimilce  akala mutane dubu 5 da 800 ne suka kasance a wannan ganggami da masu raji kishin kasa karkashin shugabancin Florian Phillipot suka shirya,yan sanda na tsare da mutane hudu yanzu haka,yayinda a fadin kasar a cewar Ministan cikin gida mutane dubu 47 ne suka hallarci taron,yan sanda na tsare da mutane  shida ga baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.