Isa ga babban shafi
Amurka-Zabe

Biden ya gabatarwa Majalisa kudirin samar da sauyi a dokar zaben Amurka

Shugaba Joe Biden na Amurka ya kama hanyar samar da sauyi a dokar ‘yancin zabe a kokarin baiwa ‘yan Majalisun jam’iyyar Democrats karfin iko da kuma rinjayen kalubalantar takwarorinsu na Republican yayin tafka muhawara a zauren majalisar Dattijan kasar a wani yunkuri na ceto Demokradiyyar kasar.

Shugaba Joe Biden na Amurka yayin jawabinsa a Atlanta.
Shugaba Joe Biden na Amurka yayin jawabinsa a Atlanta. Getty Images via AFP - MEGAN VARNER
Talla

Yayin jawabinsa a birnin Atlanta na jihar Georgia da ke yankin kudu maso gabashin kasar, Biden wanda ya bayyana rikicin Capitol na bara a matsayin yunkurin juyin mulki ya ce yanzu ne lokacin da ya dace Amurkawa su mike tsaye don baiwa zabe da demokradiyya cikakkiyar kariya.

Shugaba Biden ya kalubalanci ‘yan majalisun jam’iyyarsa ta Democrats da ke da rinjaye a zauren Majalisa kan su yi amfani da damar da suke da ita wajen goyon kudire-kudiren da ya gabatar da za su kawo gyara a zaben kasar.

Kudirin gyaran dokar zaben na Amurka ya kunshi bai wa bakar fata da sauran wadanda suka cancanci kada kuri’a a cikakkiyar damar da suka rasa a dokar zaben da kasar ke amfani da ita a yanzu.

Acewar Biden dole ne kowanne dan Majalisar Dattijai na democrats ya tsaya kai da fata wajen ganin tabbatuwar kudirin ko da bayan kada kuri’a akai.

Duk da cewa ‘ya’yan jam’iyyar Democrats 50 da ke zauren Majalisar ta dattijan ta Amurka sun kada kuri’a a kudire-kudiren na Biden biyu amma har yanzu shugaban na bukatar kuri’a 10 gabanin samun nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.